Muhimman batutuwa 11 game da Muhammad Nami, sabon shugaban hukumar FIRS
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada Muhammad M Nami a matsayin sabon shugaban hukumar tattara haraji ta Najeriya, FIRS, biyo bayan karewar wa’adin tsohon shugaban hukumar, Mista Babatunde Fowler.
Sabon shugaban FIRS, Muhammad Nami kwararren masanin ilimin harajine, kamar yadda mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu ya bayyana cikin wata sanarwa daya fitar a ranar Litinin, 9 ga watan Disamba.
Ga wasu muhimman bayanai guda 11 game da sabon shugaban FIRS, Muhammad Nami, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito:
- Kwararren masanin ilimin haraji ne, wanda yake da kwarewa a sha’anin mulki da kididdigan kudi
- Ya kwashe shekaru 30 yana aikin haraji, kididdiga, tsimi da kuma binciken kudi a bankuna, kamfanoni, gwamnati da kungiyoyi masu zaman kansu
- Kwararren mai bada shawara ne ga masu zuba hannun jari, kananan masana’antu da kuma manyan yan kasuwa
- Kwararren mashawarci ne ga kamfanoni masu siya da sayarwa da kamfanoni masu kere kere
- Ya yi karatun digiri a fannin kimiyyar zamantakewa a jami’ar Bayero ta Kano a shekarar 1991
- Ya yi karatun digiri na biyu a fannin ilimin kasuwanci a shekarar 2004 a jami’ar ABU
- Mamba ne a cibiyar haraji ta kasa, cibiyar amso basussuka, kungiyar kwararrun akantoci da sauransu
- Ya fara aiki a kamfanin PFK a shekarar 1993, inda har ya kai matakin babban mashawarci a kan haraji
- Shi ne shugaban kamfanin Manam dake Kaduna, Abuja da Neja
- A 2017 Buhari ya nada shi cikin kwamitin kwato kadarorin gwamnati da aka sace
- Yana mata da iyalai
A wani labarin kuma, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umarci babban akanta na kasa daya dinga bayyana ma yan Najeriya adadin kudaden da suke shiga lalitar gwamnatin tarayya da wanda ke fita daga lalitar a kullum.
Shugaba Buhari ya bada wannan umarni ne a ranar Litinin, 9 ga watan Disamba yayin taron kaddamar da dokoki da tsare tsaren fayyace hada hadar kudi na gwamnatin tarayya, inda ya umarci babban akantan ya wallafa rahoton duk wani kudi da aka baiwa kowacce hukuma da ma’aikata daya haura naira miliyan 10.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitnghausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa