Kasashen Afrika 10 da suka yi dacen da samun gwamnati ta gari
Babban kalubalen da kasashen Afrika ke fuskanta shine na shugabanci, nahiyar Afrika ta gaza samar da shugabannin da za a yi alfahari da irin nagartarsu kuma a yaba da salon mulkinsu.
Amma, duk da hakan, gwamnatocin wasu kasashen Afrika suna tabuka abin kirki a wasu bangarorin.
Ga jerin gwamnatocin wasu kasashen Afrika 10 da kuma bangaren da kowacce ta ciri tuta;
1. Afrika ta kudu: Duk lokacin da ake kokarin kwatanta samun cigaba a nahiyar Afrika, sai an ambaci kasar Afrika ta kudu, saboda ita ce kasar da ta fi sauran kasashen nahiyar Afrika samun cigaba.
2. Ghana: A baya ta sha fama da kalubalen tattalin arziki kafin daga baya ta fara farfadowa. Bincike ya nuna cewa kasar Ghana ta fi sauran kasashen nahiyar Afrika zaman lafiya, wanda hakan shine babban abin nasara da gwamnatin kasar ta cimma.
3. Tunisia: Kasar Tunisa ta samu yabo a matsayin kasar da tafi kowacce kasa a nahiyar Afrika tsaro.
4. Eritrea: Duk da ba kasafai ake ji duriyar kasar Eritrea ba a nahiyar Afrika, binciken masana ya nuna cewa ita ce kasar da take da karancin alkaluman aikata laifuka a tsakanin kasashen nahiyar Afrika.
5. Rwanda: Kasar Rwanda ta sha fama da rikicin kabilanci da ya yi sanadiyar mutuwar dubban mutane tare da talucewar kasar. Sai dai, duk da wadannan matsaloli da kasar Rwanda ta fuskanta a baya, gwamnatin kasar ta yi nasarar tsamo mutane miliyan guda daga kangin talauci a tsakanin shekarar 2005 zuwa 2010.
6. Botswana: Babbar gwanintar da kasar Botswana ta yi ita ce na zama kasar da ke da karancin matasalar cin hanci. Kasashen Afrika suna fama da matsalar cin hanci, lamarin da ake ganin yana daga cikin dalilan da yasa yankin ya gaza samun cigaban da ya kamace shi.
DUBA WANNAN: Arewa: Jihohi biyar da suka fi talauci a Najeriya da dalilin talaucinsu
7. Najeriya: Ita ce kasar da tafi sauran kasashen nahiyar Afrika yawan jama'a. Babban abu yabo da Najeriya ke kafafa da shi, shine kasancewarta kasar da ta fi sauran kasashen nahiyar Afrika karfin tattalin arzikin cikin gida (GDP).
8. Ethiopia: Wani abu da gwamnatin kasar Ethiopia ta yi wa sauran kasaashen nahiyar Afrika zarra da shi, shine nasarar da ta samu wajen samar da miloniyoyi cikin dan kankanin lokaci.
9. Kenya: Kasar Kenya ce kasar nahiyar Afrika ta farko da ta fara samar da wutar lantarki daga ma'adanan karkashin kasa (geothermal power).
10. Zimbabwe: A yayin da wasu kasashen ke tutiya da karfin tattalin arziki ko karfin rundunar tsaro, ita kasar Zimbabwe ta yi zarra ne a bangaren yawan matasa masu ilimi.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng