Mutane miliyan 9 na fuskantar tsananin yunwa a Afrika -Rahoto
by Azima Bashir AminuWani rahoton masana kan kamfar abincin da nahiyar Afrika ke fuskanta ya nuna cewa, kimanin mutane miliyan 9 da dubu dari 4 na tsananin bukatar agajin abinci a kasashen nahiyar musamman na yankin Sahel.
Cikin rahoton na masana da wata kungiya mai rajin tabbatar da wadatuwar abinci ta duniya tare da hadin gwiwar Majalisar Dinkin Duniya suka fitar a yau litinin, ya bayyana cewa kasashen Najeriya Nijar da kuma Burkina Faso su ne kan gaba wajen shiga halin tsaka mai wuya sanadiyyar yunwar.
Rahoton kungiyar mai zaman kanta ya bayyana cewa binciken da suka gudanar tsakankanin watan Oktoba zuwa Disamban da muke ciki, akwai mutane miliyan 9 da dubu dari 4 wadanda ke halin tsaka mau wuya kuma su ke tsananin bukatar agajin abinci.
Cikin adadin na fiye da miliyan 9 rahoton kungiyar ya nuna adadin mutane miliyan hudu da ke tsananin bukatar agajin abinci na Najeriya, yayinda Jamhuriyar Nijar ke da adadin mutane miliyan 1 da dubu dari 5 kana Burkina Faso da adadin mutum miliyan 1 da dubu dari 2.
Cikin rahoton kungiyar wadda ta fitar a yau Litinin yayin babban taronta na shekara-shekara a Faransa ta ce matukar ba a dauki matakan da suka kamata ba, akwai yiwuwar adadin mutanen da za su bukaci agajin abinci daga watan Yuni zuwa Agustan shekarar 2020 ya kai miliyan 14 da dubu dari 4 a nahiyar ta Afrika.
Rahoton kungiyar ya alakanta matsalar kamfar abincin da rikicin da yak i ci yaki cinyewa a nahiyar, baya ga sauyin yanayi da kuma gazawar shugabannin kasashen.