Ko da me kazo an fika: Wani Bakano ya canza sunansa zuwa 'Muhammadu Buhari' (Hotuna)

Wani matashin jihar Kano ya canza sunansa zuwa na shugaban kasa, Muhammadu Buhari.

Hotunan da suka yadu a kafafen ra'ayi da sada zumunta sun nuna yadda akayi bikin har da yankan rago.

Rahotannin suna bayyana cewa an gudanar da walimar ne a bayan makarantar Ado Gwaran dake titin gidan Zoo a jihar Kano

Kano, jiha mafi yawan jama'a a Arewacin Najeriya ta kasance jihar da tafi yawan masoya shugaba Muhammadu Buhari tun lokacin da yake takarar kujerar shugaban kasa.

Jihar Kano ce ta ba Buhari kuri'u mafi yawa a zaben 2015 da 2019.

A 2015 da yayi takara da tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, Buhari ya samu kuri'i 1,903,999 a Kano yayinda abokin hamayyarsa ya samu 215,779.

A 2019, Buhari ya lashe dukkan kananan hukumomi 44 na jihar Kano inda ya samu kuri'u 1,464,768 a yayinda Atiku Abubakar ya samu kuri'u 391,593.

https://netstorage-legit.akamaized.net/images/b9b2be2b77f03879.jpg?imwidth=900
Ko da me kazo an fika: Wani Bakano ya canza sunansa zuwa 'Muhammadu Buhari' (Hotuna)
Source: Facebook

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng