Macron na jagorantar taron sasanta rikicin Ukraine
by Azima Bashir Aminu, Abdurrahman Gambo AhmadYau ne shugaban Faransa Emmanuel Macron ke karbar bakoncin taron neman kawo karshen rikicin gabashin Ukraine da ya yi sanadiyar mutuwar mutane dubu 13 tun daga shekarar 2014. Ana kallon wannan taron a matsayin zakaran-gwajin- dafi ga tasirin Macron a huldarsa ta kai tsaye da Rasha.
Shugaba Macron tare da hadin gwiwar shugabar gwamnatin Jamus, Angela Merkel, zai hada shugaban Rasha Vladmir Putin da takwaransa na Ukraine Volodymyr Zelensky a wuri guda domin tattaunawar keke da keke wadda ita ce irinta ta farko a tsakaninsu.
Tuni jami’an diflomasiya suka yi gargadi danagane da sakamakon wannan zama, inda suke ganin cewa gazawa cimma matsaya, za ta yi nakasu ga tasirin Macron wanda ya shirya taron duk da zanga-zangar da ta gurgunta harkokin sufuri a Faransa.
Michel Duclos, tsohon jami’in diflomasiya kuma mamba a Cibiyar nazarin kwararru ta Montaigne da ke Faransa, ya ce, wannan taro na a matsayin zakaran gwajin dafi ga shugaba Macron da sauran Turawa, yana mai cewa, muddin shugaban ya gaza samun kayyakawan sakamako a kan Ukraine, babu shakka za a ci gaba da ware shi.
Mista Duclos na ganin cewa, shugaba Putin na Rasha zai halarci taron ne domin amfani da wata dama ta sake rarraba kawun kasashen Turai.
Macron dai na ci gaba da kokarin nuna kansa a fagen siyasar duniya a ‘yan watanni nan a daidai lokacin da kasar Jamus ta dan ja baya a harkar diflomasiya saboda shirye-shiryen uwargida Merkel na barin gado.