Masu garkuwa da mutane su neman N100m bayan sun sace Fastoci a Akure

Masu garkuwa da Bayin Allah sun yi ram da wasu Malaman addinin Kirista bayan sun dawo daga halartar wani daurin aure. Wannan mummunan abu ya faru ne kwanaki a hanyar Akure.

Daily Trust ta kawo rahoto cewa Migayun da su ka saci wadannan mutane su na neman makudan kudi kafin su sake su. Masu garkuwa da mutanen sun tuntubi coci su biya kudin fansa.

Kamar yadda mu ka samu labari, ana neman Naira miliyan 100 ne a kan Rabaren Joseph Nweke da Abokin aikinsa Felix Efobi. Masu garkuwan su ka fadawa cocinsu wannan ta wayar salula.

Wadannan Limamai sun taso ne daga Garin Awka da ke cikin Anambra domin su halarci bikin daurin aure a Ranar Akure da safe. Kafin su isa wannan biki, su ka fada a hannun Miyagun.

KU KARANTA: Wasu Miyagu sun karbe kasar nan a halin yanzu - Hajiya Buhari

An shirya wannan aure ne a Ranar Asabar, 7 ga Watan Disamban 2019 a babban jihar Ondo. Darektan yada labarai na Mabiya Darikar Katolika a jihar, Leo Aregbesola, ya sanar da hakan.

Rabaren Leo Aregbesola a madadin cocin, ya tabbatar da cewa an bukaci su biya wannan kudi kafin a saki Malaman na su da aka sace a kan titin Benin zuwa Ore a Ranar Juma’ar da ta gabata.

Kakakin ‘Yan Sanda na jihar Ondo, Femi Joseph ya tabbatar da aukuwar wannan mummunan lamari. DSP Joseph ya bayyana cewa za a baza Dakaru cikin daji domin ceto Malaman addinin.

A daidai wannan lokaci kuma mun ji cewa wasu Miyagu sun tare hanyar Abuja a karshen makon da ya wuce, inda su ka buda wuta a kan Matafiya. Wannan ya jawo mutuwar mutune hudu.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan