http://scd.ha.rfi.fr/sites/hausa.filesrfi/imagecache/rfi_16x9_1024_578/sites/images.rfi.fr/files/aefimagesnew/aef_image/images-1_0.jpg
Sojin Sudan a YemenReuters

Sudan ta janye dakarunta dubu 10 daga yakin Yemen

by

Gwamnatin Sudan ta sanar a hukumance cewa ta janye dakarunta dubu 10 da ke yaki a Yemen, inda adadinsu ya dawo dubu biyar maimakon 15.

Firaministan kasar Abdallah Hamdok ne ya sanar da haka, lokacin da yake zantawa da manema labarai a birnin Khartum bayan dawowarsa daga ziyarar da ya kai a birnin Washingon na Amurka, inda ya ce a ganinsa yaki ba zai magance rikicin kasar ta Yemen ba.

Wannan dai ne karon farko da gwamnatin kasar ta Sudan ke sanar da adadin Sojinta da ke yaki a Yemen don mara baya ga Saudiya wadda ke jagorantar gumurzun don fatattakar 'yan tawayen Houthi masu samun goyon bayan Iran.

Cikin ziyarar kwanaki 6 da Firaminista Hamdok ya kai Amurka a wani yunkuri na ganin an cire kasar daga jerin masu taimakawa ta'addanci, shugaban ya ce akwai yiwuwar kwallaiya za ta biya kudin sabulu don gyara sunan Sudan a idon duniya.

Tuni dai Amurka ta sanar da aikewa da jakada Sudan yayinda itama Sudan za ta aike da na ta jakadan matakin da ke nuna fara gyaruwar alaka tsakanin kasashen biyu.

Tun bayan da Sudan ta bayar da masauki ga Osama bin Laden jagoran kungiyar Al-Qaeda a shekarar 1993 Amurka ta sanya Kasar a jerin masu taimakawa ayyukan ta'addanci.