Yanzu-yanzu: Kotu ta baiwa Mompha beli N100m
Babban kotun tarayya dake Legas ta baiwa shahararren matashin nan mai alfahari da daloli kuma ake zargi da damfara, Ismaila Mustapha, beli.
Kotun ta baiwa matashin da akafi sani da suna 'Mompha' belin N100m.
An gurfanar da Mompha ne kan zargin damfarar N33billion.
Hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa wato EFCC ta gurfanar da Ismaila Mustapha, alias Mompha, da ake zargi da damfara a babban kotun tarayya dake jihar Legas.
EFCC na zargin Mompha da laifukan damfarar yanar gizo da safarar kudade daban-daban har 14.
Mukaddashin shugaban hukumar EFCC, Ibrahim Magu ya bayyana cewa zuwa yanzu sun kaddamar da cikakken bincike a kan Ismaila Mustapha wanda ya shahara wajen damfara da satar kudi ta yanar gizo.
DUBA NAN: Shugaba Buhari ya dira kasar Equitorial Guinea, ya halarci taron GEFC
Magu ya bayyana cewa Ismail Mustapha ya saci makudan kudade da suka kai naira biliyan 14 ta kamfaninsa mai suna Imalob Global Investment Limited, sa’annan yana amfani da asusun ajiyan kudi na banki guda 51.
A ranar 19 ga watan Oktoba, 2019, jami'an EFCC suka damke Ismail Mompha a babban filin jirgin saman Nnamdi Azikwe dake Abuja yayinda yake kokarin shilawa Dubai.
Magu yace yace Mompha ya mallaki kadarori da dama a Dubai, baya ga agoguna guda 5 da aka kwace daga hannunsa da suka kai naira miliyan 60.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng