Shugaba Buhari ya dira kasar Equitorial Guinea, ya halarci taron GEFC

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dira kasar Equatorial Guinea domin halartan taron kasashe masu fitar da iskar Gas GEFC karo na biyar dake gudana a Malabo, babbar birnin kasar.

Buhari ya tafi kasar ne a ranar Juma'a, 29 ga watan Nuwamba, 2019.

Buhari ya ya gabatar da jawabi na musamman a taron inda ya jaddada muhimmancin taron da aka fara a shekarar 2015.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu, wanda ya bayyana cewa taron na kwana daya zai samu halartar manyan kasashe masu fitar da iskar gas kamar Algeria, Egypt, Libya, Bolivia, Iran, Qatar, Rasha, UAE, Norwa, Kazakhstan, Venezuela da Trinidad & Tobago.

A shekarar 2001 aka fara kirkirar wannan taro a yayin taron ministoci da aka yi a kasar Iran, yayin da taron farko na kasashe masu arzikin iskar gas ya gudana a birnin Doha na kasar Qatar a shekarar 2011, na uku an yi shi a Iran a 2015 wanda Buhari ya halarta, wannan ne karo na farko da za’a yi a Afirka.

https://netstorage-legit.akamaized.net/images/a58090f1f562bde0.jpg?imwidth=900
Shugaba Buhari ya dira kasar Equitorial Guinea, ya halarci taron GEFC
Source: Facebook

KU KARANTA: Gwamnan jihar Plateau, Simon Lalong, ya sake doke PDP a kotun daukaka kara

Daga cikin yan rakiyar shugaba Buhari akwai ministan harkokin kasashen waje Geoffrey Onyeama, ministan man fetir, Timipre Sylva, ministan tama da karafa, Olamilekan Adegbite da shugaban hukumar NNPC, Mele Kyari.

Malam Garba Shehu ya karkare sanarwar da bayyana cewa daga Malabo shugaba Buhari zai zarce kai tsaye zuwa garin Daura na jahar Katsina inda zai yi hutun kwana 5.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki