Gwamnan jihar Plateau, Simon Lalong, ya sake doke PDP a kotun daukaka kara

Gwamnan jihar Plateau, Simon Bako Lalong, ya sake samun nasara kan jam'iyyar Peoples Democratic Party PDP da dan takararta a zaben gwamna jihar, Jeremiah Useni, a kotun daukaka kara.

Sanata Jeremiah Useni ya daukaka kara ne bayan kotun zabe ta yi watsi da karar da shigar a watan Oktoba.

Gwamna Lalong ya siffanta wannan nasara matsayin shaida da tabbacin abinda al'umman jihar suka zaba.

A jawabin da diraktan yada labaransa, Simon Macham, ya saki, Lalong yace wannan nasarar ba tashi bace kadai, innama nasara ce ga al'ummar jihar gaba daya.

Ya kara da cewa bai yi mamakin nasarar ba saboda bai taba shakkan cewa mutanen jihar sun amince da shi da jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ba.

Yace: "Wannan ba nasarata bace, innama nasara ce ga mutanen Plateau da suka bayyana amincewarsu da manufarmu."

"Kamar yadda na saba fada, ni gwamnan kowa ne, babu banbancin jam'iyyar, kabila, ko addini."

Lalong ya yi kira ga jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP) da dan takararta, Janar Jeremiah Useni su hada karfi da karfe wajen kawo cigaba jihar.

A bangare guda, matashin Najeriya, haifaffen jihar Plateau, Jerry Isaac Mallo, ya hada wata tsalaliyar mota irinta na farko a Najeriya.

Injiniyan kuma shugaban kamfanin Bennie Technologies LTD, ya kaddamar da motar mai suna Bennie Purrie ranar Alhamis a Transcorp Hilton dake Abuja.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng