To fah: Ban saci sisin kobo na jama'a ba, duk arzikin da nake da shi gumi na ne ya nemo mini - Saraki

- Tsohon shugaban majalisar dattawan Najeriya, ya koka a kan yunkurin EFCC na kwace gidanshi da ke Ilorin, jihar Kwara

- Kamar yadda tsohon shugaban majalisar dattawan ya sanar, kotu ta haramtawa EFCC din ko wata cibiya makamanciyarta da karbar mishi kadara

- Hukumar ta shigar da sabuwar karar ne a yunkurinta na tozartawa tare da take tsohuwar dokar kotun tarayyar gareta

Tsohon shugaban majalisar dattawan Najeriya, Bukola Saraki ya yi tsokaci a kan zargin hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC da take yunkurin kwace gidanshi da ke Ilorin, jihar Kwara.

Saraki ya bayyana cewa, hukumar ta shigar da kara a gaban babban kotun tarayya a ranar 27 ga watan Nuwamba, tare da bukatar kwace kadarorinshi na wucin-gadi.

A takardar da hadimin shi, Yusuf Olaniyonu ya fitar, Saraki ya kwatanta wannan yunkurin da take dokar kotun makamanciyar hakan tare da rashin biyayya ga ma’aikatar shari’a.

Saraki ya ce, “abun mamaki ne a ce hukumar yaki da rashawar da ke tunkaho da zama cibiyar da ta ginu a kan doka, ta yanke hukuncin take dokar babbar kotun tarayyar da ke Abuja”.

KU KARANTA: To fah: Dan ina fitowa a fim din Kudancin Najeriya ba yana nufin ni 'yar iska bace - Inji jaruma Amal Umar

Kamar yadda yace, kotun ta haramtawa wadanda ke karar, abokanta ko wata cibiya makamanciyarta da ta kwace, karba ko killace wata kadarar wanda ta ke kara.

A maimakon hukumar yaki da rashawa ta EFCC din ta hada sabuwar bukatarta da tsohuwar kararta ta bukatar karbar kadarorin tsohon shugaban majalisar dattawan, wanda tuni Saraki ya kalubalanci hakan a babbar kotun tarayya da ke Legas. Sai ta yanke hukuncin shigar da sabuwar kara don kokarin tozarta tsohon shugaban majalisar dattawan tare da take tsohuwar dokar kotun.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng