Yanzu-yanzu: Kotu ta tuɓe rawanin wani babban sarki mai daraja ta ɗaya a Najeriya

Kotun koli a ranar Juma'a ta soke wani sarki mai daraja ta daya a jihar Oyo, Eleruwa na Eruwa, Oba Samuel Adegbola.

Kamar yadda The Punch ta ruwaito, tun a 2013 kotun daukaka kara da ke zamanta a Ibadan ta kwace kujerar mulkin daga hannun Adegbola.

Basaraken da wasu mutane shida suka shigar da kara kan Mista James Olatunde Idowu da wasu mutane hudu bayan hukuncin da Mai shari'a Ladipo Abimbola na babban kotu jihar ya yanke a ranarv26 ga watan Janairun 2011 na cewa ba a zabi sarkin da ke kan karagar mulkin bisa ka'ida ba.

DUBA WANNAN: Babbar magana: An kama basarake da laifin garkuwa da mutane a Kaduna

A hukuncin da kotun kolin ta yanke, Mai shari'a Monica B. Dongban-Mensan ta mika godiyarta ga lauyoyin, Demilade Olaniyan da Tona Akande saboda jajircewarsu sannan ta yi watsi da karar da aka daukaka.

Mai shari'a Dongban-Mensan ta ce kotun ta gamsu da hukuncin da babban kotun jihar ta yanke a baya.

Oba Adegbola ya zama sarki ne a 1998 bayan rasuwar magabacinsa, Obas Bolanle Olaniyan a 1994.

Babban kotun tarayya ta jadada tsige shi da babban kotun jihar Oyo ta yi kan dalilin cewa zabensa da tabbatar da shi da gwamnan jihar ya yi ba bisa ka'ida bane.

Adegbola ya yi watsi da hukuncin kotun daukaka karar inda ya ce, "Babu damuwa domin lauyoyi na suna shirin daukaka karar zuwa kotun koli."

Abokin hamayyarsa, Rasheed Oyedepo ya ce kotun ta tabbatar masa da nasarar da ya samu tun shekaru 10 da suka gabata inda ya ce kotu ce gatar talaka.

Ya kuma yi kira ga gwamnatin jihar ta Oyo ta tabbatar da aiwatar da umurnin kotun kolin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng