http://scd.ha.rfi.fr/sites/hausa.filesrfi/dynimagecache/0/0/1567/885/1024/578/sites/images.rfi.fr/files/aefimagesnew/aef_image/2019-11-14t192130z_200448812_rc27bd98wpk0_rtrmadp_3_europe-macron-geopolitics_0.jpg
Shugaban Faransa Emmanuel MacronLudovic Marin / Pool via REUTERS

Kungiyar Turai na fatan shiga tattaunawar nukiliya Rasha da Amurka

by

Kungiyar tarrayar Turai na fatan shiga sahun yankuna da ya dace a dama da su dangane da lamuran tsaro, kalaman Shugaban Faransa Emmanuel Macron.
Shugaban na Faransa na fadar haka ne a wani taron hadin gwiwa da kungiyar tsaro ta Nato da ya gudana a Paris.

Shugaban na Faransa Emmanuel Macron a wata ganawa da yayi da Jens Stolenberg babban jami’in kungiyar tsaro ta NATO a Paris, ya na mai cewa babu ta yada kungiyar Turai zata mika wuya ko amincewa da yarjejeniyoyin da suka jibanci tsaron ta da manyan kasashe ba tareda ta kasance a wurin.

Daddadiyar yarjejeniyar nukiliya da tsofin Shugabanin Amurka Ronald Reagan da na Rasha na wacan lokaci Mikhail Gorbatchev suka sanya hannu a shekara ta 1987 na haramta yin amfani da duk wani makami mai cin dogon zango ko dauke da nukiliya.

Yarjejeniyar da Amurka ta rusa a watan Agusta da ya shude bayan da ta cire kanta daga cikin wannan tafiya.

Shugaban na Faransa ganin halin da aka cimma ya bukaci, mudin aka kama hanya na sake shifuda sabin ka’aidojin da suka jibanci tsaro tsakanin kungiyar tarrayar Turai da aminan ta, Tarrayar Turai na da abin fada.