Yanzu-yanzu: Dino Melaye ya kai INEC kotu

Sanata Dino Melaye ya shigar da hukumar shirya zabe INEC kara babban kotun tarayya dake Abuja domin hanata gudanar da karashen zaben Sanata mai wakiltan Kogi ta yamma.

An shirya gudanar da zaben ne gobe Asabar, 30 ga Nuwamba, 2019.

Za ku tuna cewa Dino Melaye wanda dan takarane a zaben ya mika wasu koke-kokensa ga hukumar INEC kuma ya bakuci a dage zaben.

Amma INEC ta yanke maganar karshe kan karashen zaben kujerar sanata mai wakiltan Kogi ta yamma da aka shirya gudanarwa ranar Asabar, 30 ga watan Nuwamba, 2019.

Mista. Rotimi L. Oyekanmi, Mai magana da yawun shugaban hukumar INEC, Farfesa Mahmoud Yakubu, ya bayyanawa Daily Trust cewa a Abuja cewa babu wani kwakkwarin dalilin da zai sa a dakatad da zaben ranar Asabar.

Yayinda aka tambayeshi kan kararrakin da Sanata Dino Melaye ya shigar ofishin hukumar, Rotimi Oyekanmi, ya ce kararrakin da Melaye ya shigar ba wani kwakkwarin dalili bane da zai sa a dage zaben.

Sakamakon haka, Melaye, ta hannun lauyansa ya shigar da kara domin kotu ta hana gudanar da zaben karfi da yaji.

DUBA NAN: Yanzu-yanzu: Arsenal ta sallami Kocinta, Unai Emery

Mun kawo muku cewa NEC ta sanar da ranar da za'a tsageta tsakanin Sanata Dino Melaye da Sanata Smart Adeyemi a zaben kujerar majalisar dattawa na wakiltar mazabar Kogi ta yamma.

An soke zabe a akwatuna har 53 da ke cikin rumfunan zabe 20 da ke fadin yankin Yammacin jihar Kogi a zaben karshen makon jiya. Wannan ya sa aka kashe kuri’u 43, 127 inji hukumar INEC.

Smart Adeyemi ya lashe kuri’a 80, 118 ne yayin da Dino Malaye na jam’iyyar hamayya ya tashi da 59, 548. Tazarar da ke tsakanin manyan ‘yan takarar na 20, 570 bai kai 43, 127 da aka soke ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng