Yanzu-yanzu: Arsenal ta sallami Kocinta, Unai Emery

Kungiyar Kwallon kafa a Ingila, Arsenal ta sallami kocinta, Unai Emery, wanda ya gaji Arsene Wenger ba da dadewa ba.

Shugabannin kungiyar kwallon sun sallami Unai Emery ne bayan kashin da kungiyar ta sha jiya hannun Frankfurt a gasar kofin UEFA Europa Cup.

Hakazalika sun sallameshi kan tarihi mara dadi da ya kafa na buga wasanni bakwai a jere babu nasara ko daya.

An nada tsohon dan wasan Kungiyar, Freddie Ljungberg, matsayin mai rikon kwarya.

DUBA NAN An alanta Najeriya matsayin kasa mafi noman doya a duniya

A bangare guda, kungiyar kwallon Tottenham ta sallami kocinta, Maurizio Pocchetino, sakamakon rashin nasara a wasannin baya-bayan.

Ba tare da bata lokaci ba, Tottenham ta nada tsohon kocin Manchester United, Jose Mourinho.

Shugaban kungiyar Tottenham, Daniel Levy, yayin da ya ke bayyana nadin Jose Mourinho a shafin kulob din, ya kira Kocin a matsayin gwarzon mai horaswa, wanda zai kawo cigaba.

Har ila yau, masoya kwallon kafa a fadin duniya suna kira ga shugabannin kungiyar kwallon Manchester United su raba hanya da koci Ole Gunnar Solksjaer kan rashin cin wasannin da ya kamata.

A jiya, kungiyar kwallon Asanta ta lallasa Man United 2-1 a gasar kofin Europa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng